An Caccaki Godswill Akpabio Kan Batun Kuɗaɗen Shakatawar Sanatoci Da Ya Sanar a Zaman Majalisa 

Senator Godswill Akpabio
Senator Godswill Akpabio

A ranar Litinin ne shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ya jagoranci zaman da aka tabbatar da ministocin Tinubu 45 daga cikin 48 da ya turo. Sai dai a yayin da zaman ya kusa zuwa ƙarshe, Godswill Akpabio ya yi wata magana da aka haska a bidiyo da ta janyo cece-kuce.

Wani bidiyo da ya nuna inda Akpabio ya yi maganar ba tare da lura da cewa ana kallonsa a talabijin ba.

A cikin wani ɗan gajeren bidiyo da ya yaɗu a Intanet, an ga shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio yana gabatar da jawabi bayan kamamala zaman majalisa na ranar Litinin wanda suka tabbatar da ministoci a cikinsa. Akpabio ya sanar da tafiya hutun majalisar ta dattawa zuwa ranar 26 ga watan Satumba mai kamawa.

Biyo bayan sanarwar ba da hutun da Akpabio ya yi ne kuma ya bayyana cewa, akwai wasu ‘yan kuɗaɗe da aka ware don bai wa kowane sanata damar shaƙatawa yayin hutun.

Akpabio ya yi ƙoƙarin sauya batun biyo bayan fahimta da ya yi cewa ana kallonsa kai tsaye a gidajen talabijin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here