An buƙaci wasu maniyyatan Abuja su koma gida

1687176379293
1687176379293

Wasu maniyyata aikin hajji a Najeriya, sun koka dangane da yadda aka umarci wasunsu, su koma gida, saboda ba za su samu damar zuwa aikin hajjin bana ba, duk kuwa da biyan kuɗin aikin hajjin ta hanyar adashin gata.

Maniyyatan sun ce hakan ya faru ne bayan sun kwashe makonni a sansanin mahajjata na Abuja.

Daya daga cikin maniyattan da lamarin ya shafa ta bayyana wa BBC Hausa cewa ta share fiye da kwanaki goma a sasanin alhazan babban birnin na Najeriya, amma har yanzu ba ta san makomarsu ba, sakamakon rashin wani bayani daga bangren mahukunta.

“Ga shi muna zaune ba su yi magana ba, na fara magana sai aka yanke waya, an ce min na yi hakuri na wuce gida,”

“Shi ne na ce me ya faru da za ka ce na wuce gida bayan na zauna sati uku, kuma sai a ce min na wuce gida, mene ne ya faru? Daga nan sai ya yanke waya.”

“Idan gwamnati za ta taimake mu, muna so, tunda ga shi dai dukkanmu ba mu wuce ba, muna da yawa da maza da mata.

A wani taƙaitacan labari da darekta a hukumar alhazan Najeriya, Abdullahi Magaji Harɗawa ya yi wa BBC Hausa, ya ce maniyyatan da ke wannan koke sun fito ne ba tare da an kira su ba.

Sai dai ya ce hukumar alhazan na ɗaukan mataki.

“Alhazai ne waɗanda suka yi rajista ƙarƙashin ‘tour operators’, akwai jirginsu da aka ɗaukar musu na musamman wanda zai yi jigilar su.”

“kamfanin da aka fara da su, sun zo sun fara kuma sun gaza, amma yanzu ana shirya wani jirgin da zai zo ya kwashe su.”

“Kowane jirgi akwai lokacin da yake tashi, saboda da haka idan wasu sun zo ba tare da an kira su ba, wannan su suka kawo kan su.”

Ya kuma yi alƙawarin cewa za su tabbatar cewa an kwashe dukkanin alhazan zuwa Saudiyya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here