An ƙwace tallafin karatun da aka bai wa Mmesoma Ejikeme

Anambra panel reveals how Mmesoma forged result.jpeg
Anambra panel reveals how Mmesoma forged result.jpeg

Bayan tabbatar da sakamakon jarrabawar JAMB da Mmesoma Ejikeme ta gabatar na ƙarya ne, kamfanin ƙera motoci na Innoson Group ya janye tallafin karatu na naira miliyan uku da ya bai wa matashiyar.

Ejikeme mai shekara 19 ta yi iƙirarin cewa ta ci maki 362 a jarrabawar, wanda ya sa ta zama cikin mafiya hazaƙa a jarrabawar ta wannan shekarar.

Hakan ne ya sa mamallakin kamfanin, Innocent Chukwuma, ya ba ta naira miliyan uku a matsayin tallafin karatu.

Saii dai daga baya hukumar shirya jarrabawar ta shiga manyan makarantu a Najeriya ta musanta iƙirarin matashiyar, tana mai cewa 269 ne haƙiƙanin makin da ta ci.

“…Saboda waɗannan ƙa’idojin da kuma sakamakon bincike, mun ɗauki matakin janye tallafin karatun da muka bai wa Miss Joy Mmesoma Ejikeme,” a cewar sanarwar da kamfanin ya wallafa a yau Asabar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here