An ƙara wa’adin neman aiki a hukumomin da ke ƙarƙashin CDFIB

Paramilitary Board 750x430

Hukumar kula da kukumomin Tsaro na Civil Defence, da ta gidajen Gyara hali da kuma ta jami’an kasshe gobara, da ta kula da Shige da Fice, CDFIB, ta sanar da tsawaita wa’adin ci gaba da cike damar daukar sabbin ma’aikata da ta ke yi na shekarar nan da muke ciki.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da sakatarenta Manjo Janar A.M Jibril, mai ritaya ya fitar a yau Lahadi.
Ta cikin sanarwar, hukumar ta ce, an tsara rufe shafin cike neman damar daukar ma’aikatan ne a ranar Litinin, 4 ga watan nan da muke ciki na Agusta, amma a yanzu shafin zai ci gaba da zama a bude har zuwa ranar Litinin, 11 ga Agusta.

A cewar sanarwar, an kara lokacin ne don samar da ƙarin dama ga masu neman izinin shiga cikin kowane bangare na ma’aikatun da ke karkashin hukumar.

Tun a baya dai, hukumar ta bayyana cewa masu neman aikin za su za su shiga shafinta na Intanet na https://recruitment.cdcfib.gov.ng domin cike bayanansu da yin rijista inda kuma ta jaddada cewa tsarin daukar ma’aikata “kyauta ne” kuma za a gudanar da shi bisa tafarkin “daidai da kuma gaskiya”.

Wannan sabuwar sanarwar ta zo ne kwanaki biyu bayan da hukumar ta sake ba da shawara ga masu neman aikin da suka gabatar da bayanansu kafin a inganta shafin hukumar a baya-bayannan.

Dangane da sanarwar farko mai kwanan wata na 1 ga Agusta 2025, “duk bayanan masu neman da suka kammala cike bayanan su kafin tabbatar da su a kwanan nan ana iya samun damar shiga ta https://update.cdcfib.gov.ng.” domin yin gyara

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here