Amurka ta ƙaƙabawa shugaban Zimbabwe sabbin takunkumai

Emmerson Mnangagwa, amurka, Zimbabwe, takunkumai, shugaban, kasar
Amurka ta sanya sabbin takunkumai a kan shugaban ƙasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa kan cin hanci da take haƙƙin ɗan'adam. Sabbin takunkuman sun kuma haɗa...

Amurka ta sanya sabbin takunkumai a kan shugaban ƙasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa kan cin hanci da take haƙƙin ɗan’adam.

Sabbin takunkuman sun kuma haɗa da wasu manyan jami’an gwamnatin ƙasar waɗanda ta hana taɓa kadarorinsu da ke Amurkan tare da hana su kai ziyarar ƙashin kansu ƙasar.

Karin labari: Gaza na fuskantar ƙarancin agaji da gangan – MDD

Sabbin takunkuman sun maye gurbin waɗanda aka sanyawa ƙasar ta Zimbabwe kimanin shekara 20 da suka wuce.

“Muna ci gaba da ganin yadda ake keta haddin ‘ƴan siyasa da wasu haddin da suka shafi tattalin arziki da na bil’adama.” A cewar wata sanarwa ta fadar White House.

Karin labari: ‘Yan sanda sun haramta amfani da POS ko taransifa a ofisoshinsu

“Ana harin ƙungiyoyin fararen hula tare da hana ‘ƴan siyasa sakat, ta hanyar take muhimman haƙƙoƙinsu na walwala, yayin da manyan jami’an gwamnati ke ci gaba da sace kuɗaɗe daga lalitar gwamnati don amfanin kansu,” a cewar sanarwar.

“Munanan ayyukansu na taimakawa tare da tallafawa manyan gungun masu aikata manyan laifukan cin hanci na duniya, fasakwauri da halalta kuɗin haram da ke ƙara jefa al’umomin Zimbabwe da kudancin Afrika da wasu sassan duniya.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here