Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su tabbatar an gurfanar da wadanda suka kashe wani mutum a jihar Sokoto bisa zargin kalaman ɓatanci, a gaban kuliya.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta yi Allah-wadai da kisan, ta kuma buƙaci gwamnati da ta binciki lamarin wanda ta bayyana a matsayin ‘mai ban tsoro’.
A cewar sanarwar, “Ƙaruwar kashe-kashen batanci na buƙatar ganin hukumomi su tashi tsaye wajen tabbatar da doka da mutunta haƙƙoƙin bil’adama, wadanda suka hada da ‘yancin yin addini, ra’ayi da fadin albarkacin baki.”
Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito cewa Ahmad Rufa’i mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Sakwato ya ce, a ranar Lahadi 25 ga watan Yuni ne wasu fusatattun matasa suka kashe mutumin mai suna Usman Buda, bisa zargin sa da yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammadu.
ASP Ahmad Rufa’i, ya ƙara da cewa da isar su waɗanda suka ƙona shi suka tsere daga wurin tgare da barin mutumin, inda ya rasu bayan an kai shi a asibiti.
A martanin da gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya mayar, “ya yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankulansu da bin doka da oda a kowane lokaci.”