Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya kafa kwamitin da zai binciki kisan da aka yi wa masu zanga-zanga a jihar.
Lamarin ya faru ne yayin zanga-zangar #EndBadGovernance, inda masu zanga-zangar suka buƙaci gwamnati ta kawo ƙarshen halin yunwa da ake fuskanta a ƙasar.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, Amnesty ta jaddada buƙatar gudanar da cikakken bincike kan ayyukan hukumomin tsaro da kuma waɗanda ake zargin ‘yan daba ne suka lalata zanga-zangar.
Amnesty ta yi gargaɗin cewa rashin bincike kan waɗannan kashe-kashe, da suka faru daga ranar 1 ga watan Agusta, zai haifar da matsala ga dokokin Najeriya.
Sun jaddada cewa Gwamnan jihar dole ne ya gaggauta kafa kwamitin bincike, don bincikar kashe-kashen da ake zargin jami’an tsaro sun yi a jihar.
Ƙungiyar ta kuma nuna muhimmancin kare waɗanda abin ya shafa, iyalansu daga cin zarafi, barazana, ko cutarwa ta yadda za su iya bayar da shaida ba tare da tsoro ba.