AMIS ta miƙa saƙon jaje da ta’aziyya bisa hatsarin ƴan wasan Kano

IMG 20250531 WA0006

Kungiyar malaman makarantun addinin Musulunci ta zamani watau Model Islamic Schools AMIS reshen Kano, ta jajantawa gwamnatin jihar da ma jama’ar da iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin mota da ya rutsa da ‘yan wasan Kano da suka dawo daga gasar wasannin motsa jiki ta kasa.

Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa, ta’aziyyar na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar ta AMIS na Kano Dakta Sa’eed Bello, da Sharfuddeen A. Jibril, sakataren kungiyar suka fitar yau Lahadi.

Sanarwar ta bayyana lamarin a matsayin wani mummunan iftila’i da ya jefa al’ummar Kano cikin alhini, inda ta ƙara da cewa, AMIS na miƙa ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasu da kuma gwamnatin jihar.

“Muna addu’ar Allah SWT ya jikan wadanda suka rasu, ya gafarta musu kurakurensu, ya shigar da su cikin Al-Jannah Firdaus,” in ji sanarwar.

“Muna kuma addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata cikin gaggawa, kuma Allah ya bai wa iyalai hali da hakurin jure wannan rashin da ba za a iya kwatanta wa ba.”

AMIS ta kuma yi addu’ar Allah ya kare sake faruwar irin wannan iftila’i a gaba, ya kuma bai wa jihar Kano zaman lafiya da kwanciyar hankali.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here