Gwamnatin Tarayya ta karyata ikirarin da aka yi na cewa, ambaliyar ruwan da ta afku a garin Mokwa na jihar Neja ta faru ne sakamakon ɓallewar madatsun ruwa da ke kusa.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja yau Talata, Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar muhalli, Farfesa Joseph Utsev, ya ce duka madatsun ruwa na Kainji da Jebba suna ci gaba da aiki yadda ya kamata.
“Yana da kyau a fayyace cewa ambaliyar da aka yi a Mokwa ba ta da alaka da wani ruwa da aka sako daga madatsun ruwan Kainji ko Jebba.
“Dukkanin kayayyakin wurin masu inganci ne kuma ba su da hatsari ga al’ummomin da ke kewayen wurin,” in ji ministan.
Utsev ya bayyana juyayin gwamnatin tarayya ga gwamnati da al’ummar Neja, musamman al’ummomin da iftila’in ya shafa, wanda ya faru da safiyar ranar Alhamis, 29 ga watan Mayu.
Ya kuma yaba da yadda gwamnatin jihar, da kananan hukumomi, da masu bayar da agaji suka yi gaggawar kai ɗauki ga wadanda abun ya shafa.
A cewar ministan, ambaliyar ta samo asali ne sakamakon mamakon ruwan sama wanda ya mamaye wurare da dama har ma da magudanar ruwa a garin.












































