Ali Modu Sheriff ya musanta zargin cewa mataimakin shugaban ƙasa Shettima ne ya ƙirƙiri Boko Haram

Sen Ali Modu Sheriff addressing newsmen on his APC national chairmanship aspiration in Abuja on Friday

Tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya musanta zargin cewa ya taɓa yin ikirarin cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya kirkiro ƙungiyar Boko Haram.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a birnin Abuja mai taken, “Karya da ta yi tsanani: Shettima da Ali Modu Sheriff ba sa takaddama,” Sheriff ya bayyana cewa labarin da aka wallafa ƙarya ce kuma ta ƙunshi mugunta.

Ya bayyana cewa wannan rahoto ya kasance ƙirƙira ce marar tushe wadda aka kitsa domin yaudarar jama’a, ɓata sunansa, da haifar da rikici a cikin harkokin siyasar ƙasa.

Ya ƙara da cewa bai taɓa bayar da wata hira ko tattaunawa da wani ɗan jarida ba kan batun da aka danganta masa ba.

Sheriff ya ce labarin ƙarya ne mai cike da sharri wanda ke nufin lalata gudunmawar da yake bayarwa wajen wanzar da zaman lafiya, haɗin kai, da ci gaban ƙasa tun a jihar Borno har zuwa sassan Najeriya gaba ɗaya.

Ya kuma bayyana cewa yana da cikakken kishin ƙasa da sadaukarwa wajen tabbatar da tsaro da daidaito, don haka abin takaici ne yadda wasu marasa gaskiya ke yada labaran ƙarya domin samun suna ko neman abin duniya.

Sheriff ya shawarci jama’a da kafafen yaɗa labarai su yi watsi da labarin gaba ɗaya, sannan su guji yada shi.

A cewar sa, tuni ya umarci lauyoyinsa su gano waɗanda suka yada wannan labari da kuma kafofin da suka wallafa shi, domin ɗaukar matakin shari’a idan ba su gaggauta janye shi ba.

Sheriff ya jaddada aniyarsa ta tsayawa kan gaskiya da adalci, tare da tabbatar da cewa irin wannan yaɗa labaran ƙarya ba zai wuce haka ba, don kuwa zai bi doka don ganin an hukunta masu aikata hakan.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here