ADC ta soki shirin sakin mutane 70 da ake zargin ƴan bindiga ne a Katsina

Nigeria Kidnappings Bandits deputy 458x315 1

Jam’iyyar ADC ta yi kakkausar suka tare da yin watsi da shirin gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Dikko Radda na sakin mutane 70 da ake zargin ‘yan bindiga ne da ke tsare a hannun hukumomi.

Jam’iyyar adawar ta bayyana cewa matakin yana da hatsari, ba adalci, kuma cin amanar al’ummomin da ‘yan bindiga suka addaba a kananan hukumomin da ke sahun gaba na fuskantar matsalar tsaro a jihar ne.

Da yake jawabi ga manema labarai a Katsina, kakakin jam’iyyar, Lawal Tukur Batagarawa, ya yi gargadin cewa sakin mutanen zai raunana amincewar jama’a ga yunkurin gwamnati na yaki da rashin tsaro.

Bayanan sun nuna cewa wata wasika mai taken sirri daga ma’aikatar shari’a ta jihar ta nuna cewa an fara matakan shari’a domin ganin an saki mutanen 70 da ake tsare da su, inda daraktan gurfanar da kara na gwamnati, Abdur Rahman Umar, ya nemi kwamitin sa ido kan aiwatar da dokar shari’ar laifuka ya taimaka wajen sakin su.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa gwamnatin jihar ta ce shirin na daga cikin kokarin ci gaba da yarjejeniyar zaman lafiya da wasu kungiyoyin dauke da makamai da ke aiki a jihar.

Jam’iyyar ADC ta ce aiwatar da wannan mataki zai karya gwiwar jami’an tsaro, ya raina sadaukarwar wadanda suka rasa rayukansu a bakin aiki, tare da karfafa gwiwar ‘yan ta’adda da ke addabar al’ummomin karkara, inda ta kuma sanar da kafa sabuwar shugabancinta a jihar da kuma kwamitin fadada rajista da sake tantance mambobi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here