Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane 39 da jikkatar wasu fiye da 60 sakamakon fashewar tankar man fetur a jihar Neja.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata a ƙauyen Essa da ke kan hanyar Agaie zuwa Bida a ƙaramar hukumar Katcha, bayan wata motar tankar man fetur ta kife sannan ta kama da wuta.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu mazauna yankin sun taru domin dibar man fetur daga cikin tankar kafin ta fashe.
A cikin wata sanarwa da hukumar NEMA ta fitar, ta ce bayan samun rahoton hatsarin, babbar daraktar hukumar, Zubaida Umar, ta umarci shugaban ofishin NEMA na Minna, Hussaini Isah, da ya tura tawagar agaji don taimakawa hukumar agajin gaggawa ta jihar Neja da sauran jami’ai wajen aikin ceto.
Hukumar ta bayyana cewa fashewar, wadda ta faru da misalin ƙarfe uku da rabi na rana, ta yi sanadin mutuwar mutane 39 tare da jikkata wasu fiye da 60, ciki har da maza, mata da yara.
Zubaida Umar ta jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa, tare da jan hankalin ‘yan ƙasa da su daina taruwa a wajen hatsari domin dibar man fetur, domin hakan kan janyo asarar rayuka da dukiya.
Haka kuma ta roƙi jama’a su guji taruwa a wuraren da motoci suka yi hatsari, tare da sanar da hukumomin agaji cikin gaggawa don gudanar da ayyukan ceto.
Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ya bayyana jimaminsa kan lamarin, yana mai cewa abin takaici ne yadda mutane ke ci gaba da kusantar motar tankar da ta kife duk da wayar da kai da ake yi kan hatsarin hakan.
Idan za a iya tunawa, a watan Oktoba na shekarar 2024, sama da mutum 100 suka mutu a irin wannan fashewar tankar man fetur a hanyar Kano zuwa Hadejia da ke jihar Jigawa bayan jama’a sun yi ƙoƙarin dibar man da ya zube.













































