A rage wasu ayyukan majalisar Tarayya don ƙara kuɗin a harkokin tsaro – Ali Ndume

Ali Ndume new 750x430

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ba da shawarar rage wasu ayyukan gwamnati da ba su da mahimmanci, musamman ayyukan majalisar tarayya, domin karkatar da kuɗaɗe zuwa yaki da tsaro a Najeriya.

A wata hira da aka yi da shi a shirin siyasa a gidan talabijin na Channels, Ndume ya ce ya dace a rage yawan zaman majalisa, misali a rika gudanar da zaman sau ɗaya cikin kwata, tare da daidaita alawus da wannan sabon tsarin.

Ya bayyana cewa Najeriya na kashe kuɗaɗe da yawa a wajen da ba ya amfani ga mafi yawan jama’a, ya kuma ce ya kamata gwamnati ta mai da hankali kan kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa fiye da komai.

Ya nuna damuwa kan yadda ake cigaba da kashe kuɗaɗen gudanarwa duk da cewa kasafin kuɗi na 2025 bai fara aiki ba, inda ya ce kasa da kashi biyar cikin ɗari na ‘yan Najeriya ne ke amfana da wadannan kuɗaɗe da ake warewa.

Ndume ya ce ba shi da wata fargaba idan shawarar tasa za ta haifar da sabani tsakaninsa da wasu ‘yan majalisa, yana mai cewa ya saba fuskantar matsaloli a majalisar tun da dadewa.

A bangare guda, Ndume ya yi tsokaci kan kalubalen fasaha wajen yaki da matsalar tsaro, inda ya bayyana cewa Najeriya tana da ƙarancin tauraron dan adam, kuma waɗanda ake da su ba a wadatarwa wajen sa ido da bibiyar ‘yan ta’adda cikin lokaci.

Ya ce wannan rashin kayayyakin sa ido ya sanya jami’an tsaro kasa gano wasu muhimman lamura, ciki har da rashin iya gano wani janar da ya bace a cikin wani aiki da ya gabata.

A halin da ake ciki kuwa, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan tsaro saboda yawaitar hare-hare da garkuwa da mutane a sassa daban-daban na ƙasar, tare da bada umarnin ɗaukar karin jami’an sojoji da ‘yan sanda domin karfafa tsaro.

Tinubu ya bayyana cewa za a ɗauki karin jami’an ‘yan sanda 20,000, wanda hakan zai kai adadin jami’an da ake son dauka zuwa 50,000 gaba ɗaya, tare da karfafa rundunar soji domin tinkarar barazanar tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here