Gwamnatin jihar Kano ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya ba da umarnin fitar da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero daga fadar Nasarawa da ke Kano, saboda bukatar dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Gwamnati ta yi zargin cewa wasu mutane na amfani da ci gaba da zaman sarkin a fadar Nasarawa domin rura wutar rikici a fadin jihar.
Da yake jawabi a gidan gwamnatin Kano a lokacin rabon kayan tallafin da dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tarauni Hon. Kabiru Dahiru Sule, Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya jaddada matsayin gwamnatin, inda ya yi kira ga shugaban kasa da ya sa baki.
Karin karatu: Kano: Jami’an tsaro sun tare hanyar shiga gidan Sarki na Nassarawa, sun kama ‘yan daba 17
Ya ce, ci gaba da zaman Aminu Ado a gidan Nassarawa wani yunkuri na gayya da tarwatsa zaman lafiyar gwamnantin jiha da kuma dakile yunkurin ta na yin ayyuka yadda ya kamata.












































