A Daina yi wa masu yiwa ƙasa hidima barazana don sun soki gwamnatin Tinubu – Amnesty International ta gargadi NYSC

Amnesty International

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da jami’an hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC) bisa zarginsu da aika sakonnin barazana ga wata mai yiwa ƙasa hidima da ya caccaki gwamnatin shugaba Bola Tinubu kan hauhawar farashin kayayyaki da kuma tabarbarewar tattalin arziki.

An gano matashiyar a cikin wani faifan bidiyo da aka yada a TikTok tana bayyana takaicinta kan tabarbarewar tattalin arziki a Najeriya.

Ta fito fili ta caccaki shugaba Tinubu, inda ta kira shi a matsayin “mummunan shugaba,” kuma ta yi tambaya kan irin matakan da gwamnati ke dauka na rage wa ‘yan kasa radadin talauci.

Bayan bidiyon nata ya samu karbuwa, ‘yar bautar kasa ta yi ikirarin cewa ta fara samun sakonnin barazana, da ake zargin jami’an NYSC ne ke yi mata.

Karanta: Hukumar EFCC ta kama shahararren ƴar TikTok Murja Kunya bisa zargin cin zarafin Naira

Da take mayar da martani game da lamarin, Amnesty International, a cikin wani sako ta X, a ranar Lahadi da ta fitar, ta ce maimakon yi mata barazana, ya kamata hukumomi su ba da fifiko wajen magance matsalolin tattalin arzikin kasar nan.

“Miliyoyin mutane a Najeriya na fuskantar matsanancin talauci. Ya zuwa yanzu dai mahukuntan kasar sun gaza samar da ingantattun matakan dakile ayyukan ta’addanci, lamarin da ya bar miliyoyin mutanen da suka fadda rai daga fita daga kalubalen tattalin arziki da kuma cin moriyar hakkinsu na dan Adam”.

A cewar Amnesty International “Dole ne hukumomin Najeriya su daina mayar da martani da tashin hankali da barazana ga daidaikun mutane da kungiyoyin da ke bayyana ra’ayoyinsu ba tare da mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin kasa da kasa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here