2025: Tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da kashi 4.32 cikin ɗari a zango na biyu na shekara

GDP 750x430

Tattalin arzikin Najeriya ya nuna ƙarfin juriya da ci gaba, in ji sabbin alkaluman da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar, ya bayyana cewa Jimillar haihuwar tattalin arzikin Ƙasar (GDP) ta ƙaru da kashi 4.32 cikin ɗari a zahiri, a zango na biyu na shekara ta 2025.

Wannan ƙimar ta fi wadda aka samu a zangon biyu na shekara ta 2024, wanda ya kasance kashi 3.48 cikin ɗari, da kuma zangon farko na 2025 da aka samu kashi 3.13 cikin ɗari.

A cikin zangon da ake magana a kai, fannin noma ya ƙaru da kashi 2.82 cikin ɗari, wanda ya fi kashi 2.60 cikin ɗari da aka samu a zangon biyu na shekarar 2024.

Haka kuma fannin masana’antu ya tashi da kashi 7.45 cikin ɗari daga 3.72 cikin ɗari a zango na biyu na 2024, yayin da sashen ayyuka ya samu ci gaba da kashi 3.94 cikin ɗari daga 3.83 cikin ɗari da aka samu a zangon da ya gabata.

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta bayyana cewa jimillar GDP a zangon biyu na shekarar 2025 ya kai Naira tiriliyan 100,730,501.10 a farashin asali.

Wannan ya fi Naira tiriliyan 84,484,878.46 da aka samu a zangon biyu na 2024, abin da ya nuna ƙaruwa da kashi 19.23 cikin ɗari a cikin shekara.

A bangaren tattalin arzikin da ba na man fetur ba, an samu ci gaba da kashi 3.64 cikin ɗari a zangon biyu na 2025.

Wannan ya fi kashi 3.26 cikin ɗari da aka samu a zango na biyu na 2024, da kuma kashi 3.19 cikin ɗari da aka samu a zangon farko na 2025.

Fannin ya samu turbar ci gaba daga noma, sadarwa, harkar gine-gine, harkokin kuɗi da inshora, kasuwanci, da samar da wutar lantarki.

Sai dai gudunmawar fannin da ba na man fetur ba zuwa GDP ya tsaya a kashi 95.95 cikin ɗari a zangon biyu na 2025, wanda ya yi kasa da kashi 96.49 cikin ɗari da aka samu a zangon biyu na 2024, da kuma kashi 96.03 cikin ɗari da aka samu a zangon farko na 2025.

A gefe guda kuma, fannin man fetur ya tashi da kashi 20.46 cikin ɗari idan aka kwatanta da zangon biyu na 2024, wanda ya nuna ƙaruwa mai yawa idan aka kwatanta da kashi 10.08 cikin ɗari a wancan lokaci.

Rahoton ya nuna cewa matsakaicin fitar da danyen mai a zangon biyu na shekarar 2025 ya kai ganga miliyan 1.68 a kullum, wanda ya fi ganga miliyan 1.41 da aka samu a zangon biyu na 2024 da kuma ganga miliyan 1.62 da aka samu a zangon farko na 2025.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here