Aƙalla mutane huɗu sun mutu a wani mummunan haɗarin mota da ya faru a gadar Kara da ke kan babban titin Legas zuwa Ibadan.
Rahotanni sun bayyana cewa haɗarin, wanda ya auku da yammacin Laraba, ya haɗa da manyan motoci da dama ciki har da tankar mai da suka yi karo da juna a kan gadar.
Rahotanni sun ce ɗaya daga cikin waɗanda suka mutu guda ne daga cikin matuka motocin, wanda jikinsa ya ƙone matuƙa har ba a iya ganewa.
Lamarin ya jawo cunkoso mai yawa a babban titin, inda motoci suka tsaya cak kuma fasinjoji da masu zirga-zirga suka makale.
Wasu shaidu sun ce ɗaya daga cikin motocin, wadda ke ɗauke da kaya, ta kauce daga hanya ta bugi katangar gada, abin da ya sa kan motar ya yanke ya fada cikin rafi.
Rahotanni daga shaidun da ke wurin sun nuna cewa wasu daga cikin mutanen da ke cikin motar da ta fadi cikin rafi ba a samu nasarar gano su ba har zuwa lokacin da aka tattara bayanin nan.













































