Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙaramar hukumar Birni Injiniya Sagir Ibrahim Koki, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar (NNPP), saboda rikicin cikin gida da aka gaza magancewa musamman na shugabancin jam’iyyar.
A cikin wata wasika da ya aika wa shugabar jam’iyyar NNPP ta unguwar Zaitawa a birnin Kano, mai kwanan wata 11 ga Nuwamba, 2025, Koki ya bayyana cewa matakinsa ya yi daidai da ‘yancinsa na doka kamar yadda sashe na 40 na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na 1999 (wanda aka gyara) da kuma sashe na 7.1 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar NNPP suka tanada.
Ya ce rikicin cikin gida a shugabancin jam’iyyar ya sanya masa wahala wajen ci gaba da gudanar da aikinsa yadda ya kamata, tare da wakiltar mutanen birnin Kano yadda suke fata a majalisar wakilai.
Dan majalisar, wanda ya kasance mataimakin shugaban kwamitin harkokin man fetur (bangaren rarrabawa) a majalisar wakilai, kuma abokin siyasa na Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna godiya ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi wajen yi wa al’umma hidima.
Ya kara da cewa gogewa da amincewar da ya samu a lokacin da yake wakilci karkashin jam’iyyar za su ci gaba da kasancewa abin alfahari a gare shi, tare da tabbatar wa jam’iyyar da girmamawa da godiyarsa.
Ko da yake bai bayyana matakin siyasa na gaba ba, wasu majiyoyi na kusa da shi sun ce yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki kafin ya zabi sabuwar jam’iyya gabanin zaben 2027.
Injiniya Sagir Ibrahim Koki, wanda shi ma cikakken memba ne na ƙungiyar injiniyoyi ta Nijeriya, ya lashe zabe a karkashin jam’iyyar NNPP a zaben 2023.
Murabus dinsa ya kara yawan manyan jiga-jigan da suka bar jam’iyyar a ‘yan watannin baya saboda rikicin shugabanci a matakin kasa.













































