Ɗan gwamnan Jigawa ya rasu kwana guda bayan rasuwar mahaifiyarsa

Umar Namadi 750x430 1

Dan gidan gwamnan jihar Jigawa, Abdulwahab Umar Namadi, ya rasu kwana guda baya rasuwar mahaifiyar gwamnan.

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel ya fitar, ya ce marigayin mai shekara 24 ya rasu ne ranar Alhamis da maraice, sakamakon wani mummunan hatsarin mota a kan hanyar Dutse zuwa Kafin Hausa.

Marigayin na kan hanyarsa ne ta zuwa ta’aziyyar kakarsa – wadda ta rasu a ranar Labara – lokacin da hatsarin motar ya rutsa da shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here