Ɗalibin jami’a ya rataye kansa a Najeriya

FB IMG 16743946020570287
FB IMG 16743946020570287

Wani ɗalibin jami’ar Fasaha ta tarayya da ke Akure a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya ya rataye kansa a ɗakinsa.

Rahotonni sun ce ɗalibin na aji uku a jami’ar inda yake karantar fannin fasahar zane-zanen kayayyaki.

Jaridar Punch a Najeriya ta ambato wata majiya na cewa abokan marigayin ne suka fara gano gawarsa, bayan da suke je ɗakin suka tarar da shi a kulle, suka yi magana suka ji shiru daga nan suka yanke shawarar karya ƙofar, inda suka same shi a rataye ya mutu.

Mai magana da yawun run dunar ‘yan sandan jihar Misis Funmilayo Odunlami ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ta ƙara da cewa tuni aka kai gawar ɗakin ajiye gawarwaki tare da kuma ƙaddamar da bincike domin gano abin da ya janyo ɗalibin ya rataye kansa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here