Daliban Kwalejin Kimiyya ta St. John Vianney da ke Ukwulu, a jihar Anambra, sun yi nasarar zama zakaru a gasar muhawara ta Birtaniya da Najeriya.
Makarantun da suka wakilci Najeriya sun hada da, Makarantar Britarch da Sure Start da ke Abuja sai St. Augustine’s College ta Jos da St. John Vianney Science College da ke Anambra.
Wakilan Burtaniya a gasar sun kunshi makarantar yan mata ta Central Foundation da Maghull High School da kuma Shireland High.
Gasar muhawarar wadda aka gudanar a ranar Alhamis, kungiyar Bring-It-On Africa da Debate Mate da ke Burtaniya ne suka shirya ta.
An tsara gasar ne don inganta tattaunawa tsakanin al’adu da kuma kaifin tunani da maganganu da basirar fahimtar dalibai daga kasashen biyu.
Uwar gidan Gwamnan Anambra Dakta Nonye Soludo, a cikin sakon taya murna da ta fitar ranar Asabar a Awka, ta yaba wa daliban da suka fito da jihar ta Anambra kunya a idon duniya.
Mai dakin gwamnan, wadda ta kafa gidauniyar Kiwon lafiyar Jama’a ta Healthy Living Initiative, ta kara da cewa nasarar da suka samu wata shaida ce da ke tabbatar da cewa, ilimi ya kasance ginshikin al’ummar jihar ta Anambra.
Dakta Nonye Soludo, ta kuma taya ma’aikata da jagororin gudanarwa na Kwalejin Kimiyya ta St. John Vianney murna saboda samun nasarar.
Chibueze Jennifer, Catherine Obiokafor da Benjamin Eneoli, da kuma Valentine Onwuegbusi su ne suka wakilci Anambra a gasar, tare da jagoransu, Mista John Onuigbo.













































