Ɓarayin daji sun sace mutum 56 a jihar Neja

Barayin, Daji, sace, mutum, jihar, neja
Ɓarayin daji sun sace mutum aƙalla 56 da suka ƙunshi mata da yara a ƙauyukan Kankuru, da Adogon-Mallam, da kuma Tungan-Kawo da ke yankunan ƙaramar hukumar...

Ɓarayin daji sun sace mutum aƙalla 56 da suka ƙunshi mata da yara a ƙauyukan Kankuru, da Adogon-Mallam, da kuma Tungan-Kawo da ke yankunan ƙaramar hukumar Munya da kuma Shiroro, a jihar Neja.

Bayanai sun nuna cewa an sace mutum 30 ne a ƙauyen Kankuru, a ranar Lahadi da daddare, yayin da aka sace wasu 26 a garuruwan Adogon-Mallam da Tungan-Kawo a ƙaramar hukumar Shiroro, kamar yadda jaridar BBC Hausa ta rawaito.

Karin labari: Babbar Kotu a Kano ta magantu kan shari’ar Ganduje da matarsa da wasu mutum 6

Ƙauyen Kankuru, inda aka fara sace mutanen ba shi da nisa daga Kuchi, inda aka sace mutum 150 da suka haa mata masu ciki da masu goyo da kuma yara kwanan nan.

Jaridar ta ce shugaban ƙaramar hukumar Munya, Aminu Najume, ya tabbatar da labarin, inda ya ƙara da cewa a yanzu haka akwai manoma 220 daga yankin ƙaramar hukumar da ke hannun ƴan bindiga, waɗanda ke ta buƙatarsu su biya kuɗin fansa.

Karin labari: “Zan riƙa samun sama da dala miliyan dubu 30 nan da ƙarshen 2024” – Ɗangote

Shugaban ya roƙi gwamnatin tarayya ta taimaka ta kai musu ɗauki a kan matsalar tsaron da suke fama da ita

Wasu daga cikim mazauna ƙaramar hukumar sun ce ɓarayin sun buƙaci a ba su naira miliyan 63 da babura uku da buhun shinkafa 10, kafin su saki mutanen.

Wani gungun ƴan bindigar kuma da ke riƙe da mutum 20 ya buƙaci a biya naira miliyan 10 da babura uku da buhun shinkafa 10, yayin da wani gungun kuma ke neman a ba shi Naira miliyan 53.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here