Ƴansanda a jihar Bauchi sun kama wani matashi kan zargin kashe mahaifiyarsa da taɓarya

Police Police 2233 750x430

Rundunar ƴansanda a jihar Bauchi ta ce, ta kama wani matashi kan zargin kashe mahaifiyarsa da taɓarya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar, CSP Ahmed Wakili ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne ranar 24 ga watan Fabrairu a wata unguwa mai suna Abujan Kwata.

Ya ce ana zargin matashin mai suna Safiyanu Dalhatu ɗan shekara 20, da amfani da taɓarya wajen lakaɗawa mahaifiyarsa duka har ta kai ga rasa ranta.

Karanta: Sarkin Ilorin ya bukaci Limamai su yi wa’azi kan kisan gilla

“Matashin ya yi wa mahaifiyar tasa mai suna Salama Abdullahi mai shekara 40 munanan raunuka a hannu kuma ya yi mata jina-jina abin da ya kai ga mutuwarta,” in ji sanarwar ƴansandan.

CSP Wakili ya ce bayan samun rahoton abin da faru ne suka aika tawagar jami’ansu zuwa anguwar, inda suka ɗauki mahaifiyar matashin zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa, kuma a nan ne wani likita ya tabbatar da mutuwarta.

Ya ƙara da cewa suna riƙe da matashin a halin yanzu da kuma taɓaryar da ya yi amfani da ita domin ci gaba da bincike, kuna da zarar an kammala bincike ne za su miƙa wanda ake zargin hannun kotu domin yanke masa hukunci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here