Ƴan sanda sun kama wani mutum da ake zargi da kashe kakanninsa saboda rigima kan abinci a Kano

Police olopa new 750x430

Rundunar ’yan sanda ta jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 30 mai suna Mutawakilu Ibrahim bisa zargin kashe kakanninsa bayan wata rigima da ta samo asali daga batun abinci.

Lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis a unguwar Kofar Dawanau da ke Kano, inda aka kai rahoto zuwa ofishin ’yan sanda na Dala da misalin karfe 9:30 na safe.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, an bayyana cewa wanda ake zargi ya yi cacar baki da kakanninsa, Muhammad Dansokoto mai shekaru 75 da Hadiza Tasidi mai shekaru 65, kafin daga bisani ya kai musu hari da wuka har suka samu mummunan rauni.

Rahotanni sun nuna cewa an garzaya da wadanda abin ya rutsa da su zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, inda likitoci suka tabbatar da mutuwar su.

Karin labari: Kano: ‘Yan sanda sun kama sama da mutane 100 da ake zargi da aikata laifuka cikin sabon shirin “Operation Kukan Kura”

Daga bisani an mika gawarwakin ga iyalai domin gudanar da jana’iza bisa tsarin musulunci.

Kiyawa ya ce bincike na farko ya nuna cewa mai laifin yayi kisan ne a lokacin da yake cikin maye na miyagun kwayoyi ko abin sha mai sa hankali ya gushe.

Ya kara da cewa kwamishinan ’yan sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bada umarni a mika shari’ar ga sashen binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da cikakken bincike.

Rundunar ’yan sanda ta bayyana cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala binciken.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here