Ƴan sanda sun kama Sowore a kotun Abuja

Sowore omoyele

Rundunar ‘yan sanda ta babban birnin tarayya Abuja ta kama mai rajin kare haƙƙin ɗan adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC) a zaɓen shekarar 2023, Omoyele Sowore.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama Sowore ne a ranar Alhamis a harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja, bayan ya halarci wajen domin nuna goyon baya ga shugaban haramtacciyar ƙungiyar Biafra (IPOB) da ke tsare, Nnamdi Kanu.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na ƙasa, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kama Sowore ga manema labarai, inda ya ce yana hannun ‘yan sanda kuma za a gurfanar da shi gaban kotu a yau.

An kama Sowore ne bisa zargin karya umarnin kotu da ta hana yin zanga-zanga kan neman a saki Nnamdi Kanu.

Cikakkun bayanai za su biyo baya…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here