Ƴan sanda sun kama mutane 2 da ake zargin ƴan bindiga ne tare da ƙwato alburusai 1,295 a Katsina 

Machine Gun 750x430 (2)

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne dauke da bindiga ƙirar (GPMG) da alburusai 1,063 7.62x39mm AK-47, da harsashi 232 na PKT 7.62x69mm. 

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, DCP Olumuyiwa Adejobi, ya rabawa manema labarai ranar Litinin a Katsina.

Adejobi ya ce an kama wadanda ake zargin ne a hanyar kauyen Ingawa zuwa Karkarku a jihar Katsina ranar Litinin. Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun hada da Abdussalam Muhammed mai shekaru 25 da kuma Aminu Mamman mai shekaru 23 dukkansu mazauna kauyen Baure da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Ya bayyana cewa an kama su ne biyo bayan sahihan bayanan da suka samu kan ayyukansu, wanda hakan ya sa jami’an ‘yan sandan suka yi gaggawar daukar matakin dabara.

Kano: ‘Yan sanda sun kama sama da mutane 100 da ake zargi da aikata laifuka cikin sabon shirin “Operation Kukan Kura”

“Lokacin da aka bincika motar aikinsu, Volkswagen Golf mai launin shudi mai lamba: RSH-528 BV, an gano abubuwan fashewar a boye a cikin motar; Bindigar (GPMG), harsashi 1,063 na 7.62x39mm AK-47, da harsashi 232 na 7.62x69mm PKT,” ya bayyana.

Rundunar ta bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa ana jigilar kayayyakin ne daga Hadejia a Jigawa zuwa karamar hukumar Safana ta jihar Katsina domin rabawa ga manyan masu aikata laifuka.

Adejobi ya ce a halin yanzu wadanda ake zargin suna tsare, kuma ana ci gaba da zurfafa bincike don gano inda suka nufa, da kuma alakarsu da makaman da aka kwato.

Ya ce, Sufeto-Janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun, ya yabawa yadda jami’an suka yi gaggawar mayar da martani tare da kara musu kwarin gwiwar ci gaba da gudanar da aikin.

IGP din ya nanata kudurin rundunar na wargaza duk wani nau’i na kungiyoyin masu aikata laifuka da ke aiki a fadin kasar nan. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here