Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya sun kama wasu ‘yan jarida biyu na kamfanin dillancin labarai na Faransa (AFP), yayin da suke ɗaukar rahoton zanga-zangar neman a saki Nnamdi Kanu a birnin tarayya Abuja.
An bayyana ‘yan jaridar da aka kama da suna Nick Roll, ɗan ƙasar Amurka, da kuma John Okunyomih, ɗan Najeriya mai ɗaukar bidiyo.
Rahotanni sun nuna cewa duka biyun suna a bakin otal ɗin Transcorp da ke unguwar Maitama lokacin da ‘yan sanda suka fara harba hayakin gas a kan masu zanga-zangar.
A lokacin da ma’aikatan AFP ke ɗaukar hoton yadda lamarin ke gudana, jami’an ‘yan sanda suka kai musu hari tare da ƙoƙarin cafke su da karfi, sakamakon A haka, an lalata kyamararsu sannan kuma aka kwace wayoyinsu.
Haka kuma, jami’an sun cire abin kariya da suka sanya don guje wa shakar hayakin gas.
Daga bisani an saki Nick Roll, amma John Okunyomih aka kai ofishin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda a Abuja kafin daga baya a sake shi.
Rahotanni daga jaridar TheCable sun nuna cewa ‘yan sanda sun kuma kama Aloy Ejimakor, ɗaya daga cikin lauyoyin da ke kare Nnamdi Kanu, jagoran ƙungiyar da gwamnatin tarayya ta haramta wato Ƙungiyar ‘Yan Asalin Biafra (IPOB).
Tun da farko, ‘yan sanda sun harba hayakin gas a yankin kasuwancin Abuja yayin da masu fafutuka suka fara taruwa don kaddamar da zanga-zangar, hakan ya shafi wasu fasinjoji da suke jiran motocin haya zuwa wuraren aikinsu.
Zanga-zangar ta samu jagorancin ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore, wanda shi ne mawallafin jaridar Sahara Reporters kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa.
Ana ci gaba da tsare Nnamdi Kanu tun bayan sake cafkarsa a watan Yuni na shekarar 2021, kuma yana fuskantar shari’a a babbar kotun tarayya da ke Abuja.













































