Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ta kama wata mata mai suna Maryam Atiku, ‘yar shekara 20, bisa zargin yunkurin kashe jaririyar da ta haifa ta hanyar binne ta da ranta a wani daji dake karamar hukumar Dandi a jihar.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya fitar a ranar Laraba a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, Bello M. Sani.
A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a ranar 25 ga watan Yuni, 2025, da misalin karfe 8:00 na dare, lokacin da Maryam ‘yar unguwar Nasarawa a Kamba ta haihu, inda aka ce ta daure jaririyar nadi uku a wuyan ta, sannan ta rufe bakinta, sannan ta binne ta a wani kabari mara zurfi a daji na Malam Yaro.
Sanarwar ta bayyana cewa, a ranar 26 ga watan Yuni da misalin karfe 12:30 na rana, wani manomi mai suna Alhaji Kabiru Muhammad ya gano wata kasa mai cike da rudani mai kama da sabon kabari a lokacin da yake aiki a gonarsa da ke kusa da kauyen Mallam Yaro.
Daga nan yayi kuwwa tare da taimakon mazauna kusa, aka tono jaririyar da ranta.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, nan take aka garzaya da jaririyar zuwa babban asibitin Kamba, inda aka kula da lafiyarta kuma aka ba ta shaidar cewa tana cikin koshin lafiya.
Da samun rahoton, jami’an tsaro daga sashin binciken manyan laifuka na jihar (SCID), Birnin Kebbi, sun yi gaggawar cafke wadda ake zargin. A cewar sanarwar, ta amsa laifin da ta aikata a lokacin binciken farko.
Kwamishinan ‘yan sandan, kamar yadda sanarwar ta bayyana, ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da bayyana shi a matsayin ta’addanci.
Sanarwar ta kara da cewa bayan kammala bincike an gurfanar da wadda ake zargin a gaban kuliya domin ya zama darasi ga wasu.












































