‘Ƴan Najeriya sun mayarwa da dan shugaban kasa Seyi Tinubu martani

Seyi Tinubu, Najeriya, martani, shugaban kasa
'Ƴan Najeriya sun yiwa Seyi Tinubu ɗan shugaban ƙasar Najeriya Bola Tinubu dirar mikiyar kakkausar kalamai, bayan da ya buƙaci al'umma su ƙara haƙuri da...

‘Ƴan Najeriya sun yiwa Seyi Tinubu ɗan shugaban ƙasar Najeriya Bola Tinubu dirar mikiyar kakkausar kalamai, bayan da ya buƙaci al’umma su ƙara haƙuri da mahaifinsa sanadiyyar halin da ƙasar ke ciki na matsin rayuwa.

Al’umma a Najeriya dai na cikin ƙuncin rayuwa sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi da taɓarɓarewar tsaro da karyewar darajar Naira.

A wani saƙo da ya wallafa ta shafinsa na Instagram, Seyi Tinubu ya ce “Ba abin jin daɗi ba ne yadda mutanen Najeriya ke shan wahala kan lamarin da ya kamata a ce an wuce batun shi tun a shekarar da ta gabata.

Karanta wannan: Kotu ta bada umarnin yiwa Murja gwajin kwakwalwa

“Na so a ce babu waɗannan wahalhalu da ake sha.”

Ya ƙara da cewa “Sai dai wajibi ne mu jure domin jindaɗi a nan gaba.”

Bayan wanann saƙo da ya wallafa ne ‘ƴan Najeriya da dama, musamman a shafukan sada zumunta suka mayarwa ɗan na shugaban ƙasa martani.

Shahararren mawaƙi da ake kira Charly Boy ya wallafa a shafinsa na X cewa “Seyi Tinubu na ɗaura agogon naira miliyan 350 yayin da yake cewa ƴan Najeriya su jurewa wahalar da ake ciki.”

Karanta wannan: Kamfanin AEDC ya yi barazanar yankewa fadar Shugaban Kasa wuta

A nasa martanin, tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan, wato Reuben Abati, wanda ya wallafa a shafin X cewa ya yi “Seyi na da ƙarfin halin da zai tsoma bakinsa a wannan batu? Yana tunanin wannan lamari ne na cikin iyali? Me ya sani game da juriya?”

Seyi na daga cikin ‘ƴa’ƴan shugaba Bola Ahmed Tinubu da suka fi janyo cece-kuce a Najeriya.

Ko a kwanakin baya shugaban kasa Tinubu ya buƙaci ɗan nasa da duk wani da ba’a buƙata ba da su daina shiga babban zauren taro na fadar shugaban ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here