Ƴan majalisar arewa maso gabas sun koka kan ware su a shirin noma da kiwo na gwamnatin tarayya 

Sen. Goje Danjuma

Sanatoci da ƴanmajalisar wakilai da suka fito daga arewa maso gabashin ƙasar nan sun koka dangane da yadda a cewarsu gwamnatin shugaba Bola Tinibu ta mayar da su saniyar ware a wani shirin noma da kiwo da gwamnatin ke yi da haɗin gwiwar bankin cigaban Afirka.

Ƴan majalisar sun ce yankin arewa maso gabashin Najeriya na bayar da gudunmawa a ɓangaren noma da harkokin da suka shafi kiwo, amma ga mamakinsu, sai aka zaɓi jihohi biyu a kowane yankin ƙasar biyar don cin gajiyar shirin amma su aka yi burus da yankinsu.

Karin karatu: Atiku da El-Rufa’i da Tambuwal sun ziyarci Buhari a Kaduna

Sanata Danjuma Goje shi ne shugaban ƙungiyar yan majalisar yankin arewa maso gabas ya bayyana a wata sanarwa bayan wani taron gaggawa da suka gudanar a Abuja ranar Alhamis, ‘yan majalisar wakilai daga jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba, da Yobe sun yi Allah wadai da matakin, tare da jaddada cewa an yi watsi da dimbin albarkatun noma da yankin ke da shi.

Ya ce an zaɓi jihohi takwas ne: Kano da Kaduna da Oyo da Kuros Riba da Abuja da Kwara da Ogun da Imo.

Karanta: Jami’ar KHAIRUN ta yi bikin rantsar da sabbin dalibai sama da 570

“Ba mu fahimci abin da aka yi ba, idan ana maganar noma da kiwo ne, bai kamata a ce an manta da jihohi shida na arewa maso gabas ba. Kowa ya san rawar da muke takawa a noma da kiwo, musamman shanu. To ai akwai ɓangarori shida a Najeriya, amma an raba wa ɓangarorin ba tare da yankinmu ba,” in ji shi.

Da aka ce masa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ne ya jagoranci ƙaddamar da shirin, Goje ya ce Kashim ya wakilci shugaban ƙasa ne wajen ƙaddamar da shirin, kuma shi mataimakin shugaban ƙasa ne, ba wakilin arewa maso gabas ba. Mu ne wakilan al’umma, shi ya sa majalisa na hutu, amma muka dawo domin tattauna batun.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here