Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wasu manyan jami’an hukumar kuka da kananan hukumomin jihar Kwara a kan hanyar Omu-Aran/Ilorin.
Wadanda abin ya shafa dai su ne shugabar sashin shari’a na karamar hukumar Oke-Ero, Elizabeth Arinde, da shugabar kula da ma’aikata da kuma wadanda ba a iya tantance sunansu ba.
An dai yi garkuwa da mutanen ne da yammacin ranar Juma’a.
Rahotanni sun ce a daren ranar Asabar manyan jami’an biyu na daga cikin mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a Corner Eleyin a kan hanyar Omu-Aran/Ilorin yayin da suke komawa Ilorin, babban birnin jihar, a karshen mako a ranar Juma’a, 25 ga Afrilu, 2025.
Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 5:45 na yamma, ta yadda ‘yan bindiga biyar da suka yi wa motocin masu zaman kansu kwanton bauna kafin su kai fasinjojin cikin daji.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, a madadin kwamishinan ‘yan sandan, Adekimi Ojo, a ranar Asabar.
Bayan rahoton, rundunar da hadin gwiwar sojoji da ’yan banga, sun kaddamar da wani samame cikin gaggawa, inda aka yi nasarar ceto wasu mutane biyu Ganiyu Ajayi da Kolawole Adeyemi.
“Ana ci gaba da kokarin ceto sauran biyar da aka sace tare da damke wadanda suka aikata wannan aika-aika.
“An yi kira ga mazauna garin da su kwantar da hankalinsu, su lura, da kuma bayar da goyon baya ta hanyar bayar da bayanai masu inganci ga jami’an tsaro a kan lokaci.”
Bayan afkuwar lamarin, kungiyar lauyoyin Najeriya reshen Ilorin ta fitar da sanarwar yin garkuwa da jami’ar ta Arinde a yammacin ranar Asabar.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun Shugaban NBA reshen Ilorin, SMH Kosemani, kungiyar ta ce, “Mun damu matuka da sanar da ku cewa an yi garkuwa da Barista Elizabeth Arinde, shugabar sashen shari’a a karamar hukumar Oke Ero a jihar Kwara.
“A cewar rahotanni, an sace ta ne tare da DPM na karamar hukumar a ranar Juma’a, 25 ga Afrilu, 2025, yayin da take kan hanyarta daga karamar hukumar Oke Ero zuwa Ilorin.”