Ƴan Bindiga sun sace Kansiloli 2 da Liman 1 a Zamfara

bandit 750x430

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara ta tabbatar da cewa wasu da ake zargin yan bindiga ne sun sace kansiloli biyu da kuma liman a unguwar Tsauni da ke Gusau da yammacin Laraba.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya shaida wa manema labarai ta wayar tarho cewa waɗanda aka sace sun haɗa da kansilolin Gidan Gona da Tsibiri daga ƙaramar hukumar Maradun da kuma limamin unguwar.

Ya ce an sace mutanen ne a gaban gidajensu a Tsauni da misalin ƙarfe 7:00 na yamma, jim kaɗan bayan sallar magariba.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa unguwar Tsauni na bayan hedikwatar hukumar kiyaye haddura ta tarayya (FRSC) reshen Zamfara da ke Gusau.

Unguwar ta kasance wurin zama ga ‘yan gudun hijira daga sassan da rikicin ‘yan bindiga ya shafa.

Karanta: Gwamnatin Kwara ta tabbatar da kashe gawurtaccen shugaban gungun masu garkuwa da mutane Maidawa ta hanyar amfani da jiragen yakin NAF

DSP Abubakar ya ce an tura jami’an tsaro zuwa yankin domin ceto waɗanda aka sace, tare da kira ga mazauna yankin da su rika ba da bayanai a kan lokaci don dakile irin wannan lamarin.

Shugaban ƙaramar hukumar Maradun, Sanusi Gamagiwa, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an fara sace mutum shida, amma daga bisani aka saki uku, aka tafi da kansiloli biyu da limamin unguwar.

Ya ƙara da cewa har yanzu ba a samu wani saƙo daga masu garkuwar da su ba dangane da bukatunsu.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here