A daren ranar Litinin din da ta gabata ne ‘yan bindiga suka kai wani mummunan hari a garin Morai da ke karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara, inda suka kashe wani tsohon shugaban karamar hukuma Saminu Morai da wasu mutane uku.
An kuma yi awon gaba da wasu mazauna wurin a lokacin farmakin.
Wani mazaunin unguwar da ya tabbatar da harin, inda ya bayyana shi a matsayin rashin tausayi da ban tsoro.
“’Yan bindiga sun kai hari garin Morai da ke karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara, inda suka kashe wani tsohon shugaban karamar hukumar Talata Mafara da wasu 3. An yi garkuwa da mutane da dama,” inji majiyar.
Ya kara da cewa an kai harin ne da yammacin ranar Litinin, lamarin da ya jefa garin cikin rudani.
Kashe-kashen dai ya dauki hankulan al’ummar gargajiya da na kananan hukumomi, saboda rahotanni sun bayyana cewa Sarkin Talata Mafara da kuma DPO na yankin sun halarci jana’izar wadanda aka kashen.
Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ba ta ce uffan kan lamarin ba.
SaharaReporters