Wasu yan bindiga da ke aiwatar da dokar zaman-gida a daren Juma’a, sun kai hari a kasuwar Amaraku da ke karamar hukumar Isiala Mbano a jihar Imo.
Ko da ya ke, ba a samu asarar rai ba a harin, Kamfanin Dillancin Labarai Kasa ya tattaro cewa ‘yan bindigar da ake zargin ‘yan haramtacciyar kungiyar IPOB ne, sun kona babura uku da motoci.
Haka kuma, maharan sun lalata wasu kayayyaki da kadarori na kananan ‘yan kasuwa, wadanda galibinsu mata ne.
Wani shaidar gani da ido ya shaidawa NAN cewa ‘yan bindigar sun kuma kai hari a unguwar Obolo dake karamar hukumar.
“’Yan bindigar sun fusata ne da ‘yan kasuwa da masu safarar kayayyaki saboda karya dokar.
“Maharan sun gargadi ‘yan kasuwar da su rufe shaguna kuma kada su karya doka, suna masu gargadin kada su fito ranar Asabar.
“Sun ci gaba da kona wani bangare na kasuwar tare da kona motoci,” in ji majiyar.