Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta tabbatar da cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun ƙone wani ofishin ’yan sanda tare da wani ɓangare na wata coci a al’ummar Agwara da ke jihar, a safiyar ranar Lahadi.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a Minna, inda ya bayyana cewa harin ya faru da misalin ƙarfe 3:40 na dare lokacin da ’yan bindigar suka kai farma daki ofishin ’yan sandan Agwara.
Ya bayyana cewa tawagar ’yan sanda ta musamman da ke bakin aiki ta fafata da maharan, sai dai daga bisani ’yan bindigar suka rinjayi jami’an tsaron, inda suka yi amfani da abin da ake zargin bam ne wajen ƙona ofishin ’yan sandan.
Bayan haka, maharan sun nufi cocin United Methodist Church da ke cikin al’ummar, inda suka ƙona wani ɓangare na ginin cocin kafin su ci gaba da kai hare-hare a wasu sassan yankin.
Rundunar ’yan sandan ta kuma bayyana cewa ’yan bindigar sun sace kimanin mutane biyar a yayin harin, inda har yanzu ba a tantance sunayen mutanen da aka sace ba.
Sanarwar ta bayyana cewa ana ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki, kuma za a sanar da jama’a duk wani sabon bayani da zarar an samu.
Haka kuma, hukumomin tsaro sun fara gudanar da bincike tare da ƙara kaimi wajen farautar wadanda suka aikata laifin da kuma ceto mutanen da aka sace.
NAN













































