Al’ummomi a ƙananan hukumomin Shanono, Bagwai da Tsanyawa a jihar Kano na ci gaba da fuskantar hare-hare da sace-sace daga ‘yan bindiga duk da kasancewar jami’an tsaro masu manyan makamai a yankunan.
Shugaban kwamitin tsaro na Faruruwa a ƙaramar hukumar Shanono, Alhaji Yahya Bagobiri, ya bayyana cewa lamarin da cewa ya ta’azzara cikin mako guda, inda aka samu rahotannin hare-hare da dama a yankunan uku.
Ya ce an sace mutane da dama, kuma an kashe wani mutum a gidansa yayin da aka yi garkuwa da ‘ya’yansa, lamarin da ya kara tayar da hankalin mazauna yankin.
Bagobiri ya bayyana cewa mutane da yawa sun tsere daga gidajensu saboda tsoro, yayin da wasu da ke zama a wajen ƙauyukan suka daina ziyartar iyalansu.
Ya ce duk da kasancewar sojoji da ‘yan sanda da jami’an tsaron farar hula a yankin, akwai bukatar sabuwar dabara saboda ‘yan bindigar na amfani da hanyoyi daban-daban wajen kutsawa cikin yankuna.
Ya roƙi shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf su gaggauta ɗaukar mataki, inda ya gargadi cewa rashin yin haka zai iya janyo matsanancin tashin hankali.
Ya kuma ce, ‘yan bindigar na ƙoƙarin mamaye Shanono, Tsanyawa, Bagwai, Gwarzo da Bichi domin su kewaye Kano gaba ɗaya da hare-hare.
Hakazalika, hakimin Faruruwa a ƙaramar hukumar Shanono, Mustapha Abubakar, ya bayyana cewa lamarin ya zama abin tsoro, inda aka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da mata da yara a kwanakin baya.
Ya ce, ko a daren Juma’a a ƙauyukan Yancibi da Kadami an kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu.
Abubakar ya bayyana cewa ‘yan bindigar na shigowa daga jihar Katsina, inda suke samun sauƙin sanya ido saboda yarjejeniyar sulhu da wasu shugabannin yankin.
Ya bukaci jami’an tsaro su canza dabarar aikin su, su mamaye dazuka da hanyoyin da masu laifin ke bi domin hana su sake kai hare-hare.













































