Ɗaruruwan masu zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Abuja sun nufi majalisar dokokin ƙasar, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC, kwamared Joe Ajeoro ne yake jagorantar zanga-zangar.
Wakilin BBC Hausa da ke inda ake zanga-zangar ya rawaito cewa jami’an tsaro da suka haɗa da ‘ƴan sanda da na Civil Defense na ƙoƙarin hana su shiga harabar majalisar.
Karin labari: Gobara ta kone shaguna 50 a kasuwar ‘yan katako a jihar Kano
Sai dai a cewar wakilin duk da turjiyar da jami’an tsaro suka nuna don hana ‘ƴan ƙwadagon shiga harabar majalisar, hakan bai hana su ture shingen da aka saka ba inda suka shiga da ƙarfi sakamakon yawan da suke da shi.
Masu zanga-zangar dai sun toshe manyan hanyoyin da suka haɗa tsakiyar birnin tarayya Abuja.
Sun fara taruwa ne a hedikwatar NLC a Abuja inda a yanzu suka nufi majalisar dokokin ƙasar.