Ƙungiyar tawaye da juyin mulkin sojoji ta ɓulla a Nijar

Niger ex rebel leader Boula moves against coup plotters forms resistance group.jpeg
Niger ex rebel leader Boula moves against coup plotters forms resistance group.jpeg

Wani tsohon jagoran ‘yan tawaye kuma ɗan siyasa a Nijar ya ce ya kafa wata ƙungiya a ƙoƙarin mayar da hamɓararren Shugaba Mohamed Bazoum kan karagar mulki.

Rhissa Ag Boula ya ce ƙungiyar tasa mai suna Majalisar Nuna Bijirewa don Tabbatar da Jamhuriya (Conseil de la Résistance Pour la République) za ta tallafa wa ƙoƙarin dawo da gwamnati mai aiki da tsarin mulki a Nijar.

Wannan ita ce alama ta farko mai nuna ɓullar gwagwarmayar nuna turjiya ga juyin mulkin da sojoji a cikin gida.

An jiyo Mallam Rhissa Ag Boula, jim kaɗan bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli yana kira ga Ƙabilun Larabawa, Abzinawa da Toubawa su ɗauki makamai don mayar da Nijar kan tsarin dimokraɗiyya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here