Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta haramta safarar fatar jaki

kungiya, tarayya, afrika, safarar, fatar jaki
Ƙungiyoyin ba da agaji ga dabbobi sun yi maraba da dokar haramta safarar fatar jaki da aka kafa a faɗin Afirka. Wannan dokar dai ta haramta yanka jakai a...

Ƙungiyoyin ba da agaji ga dabbobi sun yi maraba da dokar haramta safarar fatar jaki da aka kafa a faɗin Afirka.

Wannan dokar dai ta haramta yanka jakai a ƙasashe 55 na Afrika.

Shugabannin kasashen Afirka sun amince da haramcin ne a karshen taron kungiyar Tarayyar Afirka da aka kammala a kasar Habasha ranar Lahadi.

Dakta Onyango ya bayyana cewa haramcin zai kare jakai da kuma rayuwar miliyoyin da suka dogara da su.

Karanta wannan: “Babu sakamako a binciken mutuwar Navalny” – Kremlin

Buƙatar fatar jakan dai na da nasaba da shaharar wani maganin gargajiya da ake yi da fatar jaki me suna Ejiao a ƙasar China.

Wasu sun yi imanin Ejiao yana da fa’idodin hana tsufa da kuma lafiyar jiki, koda yake wannan ba shi da tabbas.

Wata ƙungiyar agaji mai suna The donkey sactuary ta kira wannan sana’ar na saye da saya da fatar jaki a matsayin mummuna da rashin dorewa, inda ta ce sana’ar ta yi sanadin raguwar jakai a faɗin duniya musamman a kasashen Afirka da Kudancin Amurka.

Karanta wannan: ‘Yan Bindiga sun kai hari ofishin ‘Yan Sanda tare da kashe mutum 7 a Zamfara

Kimanin kashi biyu bisa uku na adadin jakai miliyan 53 na duniya ana kiyasin suna Afirka ne.

Ana kallon haramcin a matsayin wani muhimmin mataki na kiyaye wadannan dabbobi da kuma tallafawa al’ummomin karkara da suka dogara da su don jigilar kayayyaki da kuma ayyukansu na yau da kullum.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here