Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da iskar Gas ta ƙasa (NUPENG) ta ayyana Sanata Adams Oshiomhole a matsayin wanda ba a maraba da shi a tsakanin ma’aikatan man fetur da gas a ƙasar, bayan suka da ya yi wa ƙungiyar (PENGASSAN) saboda yajin aikin ta na goyon bayan ma’aikata 800 da kamfanin Matatar Man Dangote ya sallama.
A cikin hirar da ya yi da tashar Arise TV a ranar 3 ga Oktoba, Oshiomhole ya soki PENGASSAN saboda ya mayar da sabanin ta da kamfanin Dangote zuwa yajin aiki na ƙasa baki ɗaya, yana cewa wannan mataki ne na gaggawa kuma bai dace ba da sauran ma’aikata.
A cikin wata sanarwa da shugaban NUPENG, Williams Akporeha, da sakatare janar Afolabi Olawale suka sa hannu, ƙungiyar ta bayyana takaicinta kan maganganun Oshiomhole, tare da ayyana shi a matsayin wanda ba a maraba da shi a tsakanin ma’aikatan man fetur da gas.
Sanarwar ta ce wannan mataki na nufin daga yanzu NUPENG ba za ta halarci ko bayar da goyon baya ga duk wani taro ko abin da ya haɗa da Oshiomhole ba, tana roƙon ƙungiyoyin NLC, TUC, da sauran ƙungiyoyin farar hula masu kishin gaskiya su lura da hakan.
Ƙungiyar ta bayyana kalaman Oshiomhole a matsayin cin amanar ƙa’idojin ƙwadago da kuma rashin mutunta dokokin ƙasa da na ƙungiyar ƙwadago ta duniya (ILO).
NUPENG ta bayyana takaici cewa tsohon jagoran ƙwadago ya koma mai goyon bayan zaluncin kamfanoni, yana ƙoƙarin halatta korar ma’aikata da suka yi amfani da haƙƙinsu na haɗuwa da yin yajin aiki cikin lumana.
Karin labari: Kar ku kawo cikas ga matatar Dangote – Shettima ya faɗawa PENGASSAN
Ƙungiyar ta ce Oshiomhole ya ci amanar ma’aikatan Najeriya ta hanyar yin shiru game da korar ma’aikata sama da 800 a kamfanin Dangote, amma ya soki yajin aikin PENGASSAN da aka yi don kare haƙƙinsu.
Ta jaddada cewa bisa Sashe na 31 na dokar ƙungiyoyin ma’aikata (Trade Unions Act Cap T14 LFN 2004), duk wani yajin aiki da aka yi cikin goyon bayan wani ɓangare na ma’aikata yana da halaltaccen tushe.
NUPENG ta ƙara da cewa hujjar Oshiomhole na cewa yajin aikin zai cutar da tattalin arzikin ƙasa, hujja ce da ake yawan amfani da ita wajen hana ma’aikata neman haƙƙinsu, wanda shi kansa Oshiomhole ya taɓa yin adawa da ita a baya.
Ƙungiyar ta tabbatar da cikakken goyon bayanta ga PENGASSAN da ma’aikata 800 da aka sallama ba bisa ƙa’ida ba, tare da alkawarin ci gaba da amfani da dukkan hanyoyin doka da ƙa’idar ƙwadago domin tabbatar da adalci.
A ƙarshe, NUPENG ta shawarci Oshiomhole da ya daina yin tsokaci kan batutuwan ƙwadago, tana cewa ya rasa duka haƙƙin ɗabi’a da cancanta wajen wakiltar muradun ma’aikatan Najeriya, musamman na fannin man fetur da gas.













































