Ƙungiyar Likitoci ta dakatar da yajin aikin da take yi a ƙasa

Doctors NARD 750x430

Majalisar zartarwa ta ƙasa ta ƙungiyar likitoci masu nemann kwarewa ta ƙasa ta dakatar da yajin aikinta na sai Baba-ta-gani da ta gudanar na tsawon makonni huɗu bayan zaman sulhu da aka gudanar da gwamnatin tarayya tare da rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna.

Shugaban ƙungiyar, Dakta Mohammad Suleiman, ya bayyana cewa dakatarwar ta bai wa gwamnati damar aiwatar da muhimman abubuwan da ba a kammala ba a cikin bukatun ƙungiyar guda goma sha tara, tare da tabbatar da ci gaba da tattaunawa ba tare da cutar da jin daɗin mambobi ba.

Ya ce duk da cewa an samu ci gaba ta fuskar yarjejeniyar da aka cimma, akwai wasu muhimman batutuwa da ke bukatar aiwatarwa, ciki har da biyan bashin haɓakar matsayi da bashin albashi, wanda gwamnati ta ɗauki alhakin kammala su cikin makonni huɗu.

Labari mai alaƙa: Ƙungiyar Likitoci ta fara yajin aiki a fadin ƙasa

Ya kuma tabbatar da aiwatar da alawus na musamman, tare da fara shirye-shiryen aiwatar da alawus na horaswar ƙwararru da warware matsalolin matakin shiga aiki da sauran alawus da suka shafi likitocin.

Ƙungiyar ta ce batutuwan da suka dade suna jiran mafita, kamar batun ma’aikatan Lokoja 5, za a kammala su cikin makonni biyu, baya ga gyaran biyan alawus 25/35, alawus na kayan aiki, da sakin kudin horaswa.

Haka kuma shugabannin asibitoci sun samu umarni su cire sharuddan da ke cutar da ma’aikata a kwangilolin wucin gadi.

Kwamitoci kan ɗaukar ma’aikatan wucin gadi da iyakar awanni za su gabatar da tsare-tsaren aiki cikin watanni biyu, yayin da tattaunawar yarjejeniyar albashi da batutuwan da suka shafi matsayin masana ga sauran ma’aikatan lafiya za su fara nan kusa.

Ƙungiyar ta bayyana cewa za ta yi amfani da makonni huɗu wajen ƙara matsa lamba da wayar da kan al’umma da gwamnati domin ganin an kammala dukkan abubuwan da suka rage, tare da kira ga mambobinta da su kasance cikin shiri muddin ba a cika abin da aka alƙawarta ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here