Ƙungiyar Lauyoyi NBA ta nuna damuwa kan saɓanin hukuncin kotuna

NBA NBA

Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta bayyana damuwa kan yadda ake samun sabani a cikin hukuncin kotuna a ƙasar.

Kungiyar ta kuma soki yadda ɓangaren zartarwa ke yin kwangila a madadin bangaren shari’a, lamarin da ta ce yana tauye cikakken ’yancin shari’a.

Reshen Akure na kungiyar ya bayyana cewa ya kamata jam’iyyun siyasa su fuskanci hukunci idan suka karya ka’idojin Dimokuraɗiyya.

Shugaban reshen Akure na NBA, Alhaji Friday Umar, ya bayyana cewa bambance-bambancen fahimtar alkalai ne kan sa ana samun hukuncin da ke sabawa juna, yana mai ƙara da cewa majalisar kula da shari’a ta ƙasa (NJC) na ƙoƙari wajen dakile wannan matsala.

Ya bayyana cewa majalisar NJC ta ƙirƙiro ƙa’idoji don hana matsalar neman kotu mai tausayi, inda masu shari’a ke ƙaura daga yanki zuwa wani domin samun alkali mai ra’ayin su.

Umar ya kuma yaba wa gwamnatin jihar Ondo bisa gina sabon ginin shari’a da aka sanya wa sunan tsohon gwamnan marigayi Oluwarotimi Akeredolu, amma ya nanata cewa irin wannan aikin ya kamata ya kasance karkashin ikon shari’a domin kare ’yancinta.

Ya ce wannan tsarin da gwamna ke bayar da kwangila don gina kotuna ko sayen motoci ga alkalan jiha yana tauye ikon shari’a.

Umar ya bayyana cewa bikin makon doka na bana zai gudana bisa taken “Najeriya: Neman shari’a mai amfani da rawar da ɓangarori ke takawa,” inda tsohon ministan sufurin jiragen sama, Alhaji Femi Fani-Kayode, zai gabatar da jawabi na musamman.

Haka kuma, za a gudanar da zama kan “Ƙarfafa adalci a zaɓe ta hanyar tsarin doka da shari’a,” ƙarƙashin jagorancin Dr. Remi Olatubora (SAN), tare da Olumide Olujimi (SAN) da Adamson Adeboro (SAN) a matsayin masu tattaunawa.

Umar ya bayyana cewa don dimokuraɗiyya ta bunƙasa, wajibi ne shari’a ta riƙa bayar da hukunci cikin gaskiya da adalci, yana mai ƙara da cewa adalcin zaɓe yana da muhimmanci domin idan tsarin ya gaza, gwamnati da ta fito daga gare ta ma za ta gaza.

Ya kuma ce, sakamakon taron makon dokar zai ƙunshi shawarwari da za su taimaka wajen ƙarfafa tsarin zaɓe da na shari’a a ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here