Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta ce ba za ta iya daukar matsaya kan dokar ta-bacin da Shugaba Bola Tinubu ya kafa a Jihar Rivers ba, inda ta jaddada matsayin ta a matsayin wani dandali na inganta manufofin bai daya da kuma hada kai don ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
A cikin wata sanarwa a ranar Asabar da babban daraktan kungiyar ta NGF, Abdulateef Shittu ya fitar, ya ce daukar matsaya kan batutuwan bangaranci, ba tare da la’akari da yadda aka yi magana ba, yana nuna rashin fahimta.
Jihar Rivers dai ta fuskanci tabarbarewar harkokin siyasa kusan shekaru biyu, inda tsohon gwamna Nyesom Wike da magajinsa, Sim Fubara ke fafatawa a kan karagar mulki, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.
A martaninsa, Tinubu ya kafa dokar ta baci a jihar a ranar Talata, inda ya dakatar da Fubara ds mataimakiyarsa Ngozi Odu, da daukacin ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
Karin karatu: Dattawan arewa sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara bakin aiki
A martanin da ta mayar, NGF ta bukaci jama’a da kafafen yada labarai da su kasance masu fahimta, tare da bayyana kwarin gwiwar cewa ingantattun tsare-tsare da matakan magance rikice-rikice za su magance duk wata matsala.