Ƙungiyar gwamnonin Arewa ta bayyana alhini bisa rasuwar Aminu Dantata

WhatsApp Image 2025 06 28 at 06.37.29 720x430.jpeg

Gwamnonin Arewa sun bayyana alhininsu dangane da rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu yana da shekaru 94 a duniya.

Shugaban kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, a yau Asabar a saƙon ta’aziyya a madadin takwarorinsa, ya bayyana rasuwar attajirin wanda haifaffen Kano ne a matsayin babban rashi a ƙasa baki ɗaya.

Yahaya, ta bakin Babban Daraktan yaɗa labarai na gidan Gwamnatin Gombe, Ismaila Misilli, ya bayyana cewa marigayin ya kasance ɗaya daga cikin hamshaƙan attajirai da ake girmamawa a Afirka.

Ya ƙara da cewa, Alhaji Aminu Dantata ya kasance jigo a tarihin tattalin arzikin Najeriya wanda ya kasance daya daga cikin jagororin masu hangen nesa da suka himmatu wajen samar da kasuwanci da ci gaba da inganta rayuwar Dan-adam, ya kara da cewa, “Gudunmawar da Alhaji Aminu Dantata ya bayar wajen kawo sauyi ga tattalin arzikin Arewacin Najeriya da kasa baki daya, abu ne mai matukar muhimmanci kuma mai ɗorewa.

Shugaban na ƙungiyar gwamnonin Arewa NSGF ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga iyalan Dantata da gwamnati da al’ummar jihar Kano da ma kasa baki ɗaya.

Haka kuma, ya roƙi Allah maɗaukakin Sarki da ya gafarta masa kurakuran sa, ya kuma saka masa da Aljannatul Firdaus.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here