Ƙungiyar Editoci ta ƙasa ta ɗage taronta na shekara, Tinubu zai halarta

NGE NGE

Ƙungiyar Editoci ta Nijeriya ta sanar da ɗage taronta na shekara da ake kira All Nigeria Editors Conference (ANEC) zuwa ranakun 12 da 13 ga watan Nuwamba 2025 a birnin Abuja.

Ƙungiyar ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya tabbatar da halartar taron, kuma shi ne zai buɗe zaman taron a hukumance.

A cewar sanarwar da shugaban ƙungiyar, Eze Anaba, da sakataren ta, Onuoha Ukeh, suka fitar, dage taron ya biyo bayan wasu dalilai da suka wuce ikon ƙungiyar.

Ƙungiyar ta nemi afuwa daga mambobinta da baƙi da sauran jama’a bisa canjin ranar da ka iya haifar musu da wata matsala.

Ƙungiyar ta tabbatar cewa wurin taron zai kasance a Abuja kamar yadda aka tsara tun farko, inda ta bayyana cewa taron zai zama wata muhimmiyar dama don tattauna batutuwan da za su taimaka wajen ci gaban ƙasa da daidaituwar al’umma.

Taken taron na bana zai kasance, Mulkin Dimokuraɗiyya da Haɗin Kan Ƙasa: Rawar da Editoci ke Takawa,” yayin da taken ƙari ke cewa “Amincin Zaɓe da Rashin Amincewa: Abin da ƴan Nijeriya ke sa ran ganin a Shekarar 2027.”

Za a gabatar da manyan jawaban ilimi daga masana kamar Farfesa Awa Kalu, wanda zai yi bayani kan “Rikicin Zaɓe da Amincin Kotuna,” da Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim daga Jami’ar Abuja, wanda zai tattauna kan “Halin Ƙasa: Buƙatar Sauye-sauyen Tattalin Arziki da Siyasa.”

Haka kuma za a gabatar da jawabi kan “Sauyin Fuskokin Jarida: Yaƙi da Labaran Ƙarya, Tasirin amfani da fasahar (AI), da Matsalar Gaskiya,” daga Farfesa Abiodun Adeniyi, da kuma “Jarida, Ta’addanci da Tsaron Ƙasa” daga Janar Lucky Irabor (mai ritaya).

Ƙungiyar ta ce a rana ta biyu za a gudanar da zaman musamman tsakanin editoci da manyan jami’an gwamnati da shugabannin kamfanoni, don tattauna hanyoyin da jaridu za su taimaka wajen gina ƙasa ta hanyar aikin jarida mai ɗawainiya da gaskiya.

An bayyana cewa fiye da editoci 500 ake sa ran za su halarta daga sassa daban-daban na ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here