Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta gargaɗi gwamnatin tarayya da ta yi amfani da ragowar kwana goma daga cikin wa’adin wata guda da aka ba ta, domin warware matsalolin da ke tsakaninsu gaba ɗaya.
Wannan sanarwar ta fito ne daga taron majalisar zartarwa ta ƙasa ta ASUU da aka gudanar a jami’ar jihar Taraba da ke Jalingo, tsakanin ranakun 8 zuwa 9 ga watan Nuwamba, cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ya fitar a ranar Laraba.
Kungiyar ta bayyana cewa wasu jami’an gwamnati na yin kalaman da ke iya kawo cikas ga tattaunawar saboda suna yin kuskuren fassara game da tayin gwamnati da matsayin aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma.
ASUU ta jaddada cewa ta dakatar da yajin aikin gargadi na makonni biyu a ranar 22 ga watan Oktoba, inda ta bai wa gwamnatin tarayya wata guda don cika bukatunta kafin ranar 22 ga Nuwamba, wanda ke ƙarewa nan da kwanaki kaɗan.
Daga cikin bukatun da kungiyar ta gabatar har da sake nazarin yarjejeniyar ASUU da gwamnatin tarayya ta shekarar 2009, biyan albashin da aka rike da kuma kudaden alawus, da fitar da kuɗin farfaɗo da jami’o’i.
Kungiyar ta gargadi cewa za ta koma yajin aiki ba tare da wani sabon gargadi ba idan gwamnati ta kasa ɗaukar mataki mai ma’ana kafin wa’adin ya cika.
ASUU ta kuma shawarci gwamnati da ta ɗauki cikakken mataki na magance matsalolin da ke shafar rayuwa da yanayin aiki na malamai, tana mai cewa tayin albashin da aka gabatar mata bai dace ba.
Kungiyar ta ƙaryata ikirarin gwamnati na cewa babu isassun kuɗi don aiwatar da yarjejeniyoyin, tana mai cewa matsalar ita ce rashin ƙuduri da kishin ilimi, ba matsalar tattalin arziki ba.
ASUU ta roƙi sarakunan gargajiya, shugabanni, ɗalibai, ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC), da ƙungiyoyin farar hula da su ci gaba da matsa wa gwamnati lamba domin ta cika alƙawuranta da kuma tabbatar da biyan malamai albashi mai gamsarwa.













































