Ƙungiyar ɗalibai NANS ta yi barazanar yiwa hukumar FRSC ƙawanya

National Association of Nigerian Students NANS 640x430

Kungiyar dalibai ta kasa (NANS), a ranar Talata, ta yi barazanar bijirewa duk wani umarni na hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) bayan da ta bada umarnin kama motocin Ƙungiyar.

Kungiyar daliban ta ce ta samu matukar bacin rai da sanarwar da shugaban hukumar Shehu Mohammed,ya bayar, inda ya umurci jami’an sa da su kamo wasu motoci mallakar NANS.

Ƙarin karatu: Haɗarin mota ya kashe mutane 28 sakamakon gudun wuce sa’a a jihar Ondo- FRSC

A wata sanarwa da magatakardan majalisar dattawa a hedikwatar NANS ta kasa, Oladimeji Uthman ya sanya wa hannu ta ce umarnin kama motocin NANS ba kawai rashin mutuntawa ba ne, har ma da cin fuska ga tsarin tafiyar da aiki.

Uthman ya yi gargadin cewa “Idan duk wata rundunar FRSC ta ci gaba da aiwatar da wannan umarni na rashin adalci ta hanyar kama motocin NANS a matakin kasa ko shiyya, to kuwa za mu gabatar da gagarumar zanga-zangar kare hakkinmu. Ba za mu yarda da duk wani nau’i na rashin girmamawa ga ƙungiyarmu ba”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here