Kasar Saudiyya, ta sanar a hukumance cewa an ga jinjirin watan Zul-Hijjah na shekara ta 1446 a yammacin yau Talata.
Kamar yadda aka gani, watan Musulunci na Zul-Hijja zai fara ne a ranar Laraba 28 ga watan Mayu.
Kamar yadda kalandar Musulunci ta nuna, za a gudanar da Idin babbar Sallah na bana ne a ranar Juma’a 6 ga watan Yuni.
Hukumar kula da al’amuran Masallatan Harami da aikin Hajji da Umarah ta ƙasar Saudiyya ce ta sanar da hakan a shafinta na X a yammacin yau Talata.












































