Ƙasar Saudi Arabiya ta rage wa Najeriya guraben aikin Hajji na shekarar 2026 – NAHCON

NAHCON Chairman Prof Abdullahi Saleh Usman sabo 750x430

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa hukumomin Saudiyya sun amince da kujeru 66,910 ne kawai domin mahajjatan Najeriya a aikin Hajjin shekarar 2026.

Hukumar ta ce Saudiyya ta sanya wannan adadi a shafin NUSUK Masar saboda rashin cikakken amfani da kujeru 95,000 da aka bai wa Najeriya a bara.

Wannan bayani ya fito ne daga wata sanarwa da mataimakiyar darakta a sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na hukumar, Hajiya Fatima Usara, ta fitar a birnin Abuja ranar Alhamis.

A cewar kwamishinan ayyuka na NAHCON, Yarima Anofiu Elegushi, ƙasashen Saudiyya sun tanadar da kujeru 66,910 ga mahajjatan Najeriya a shafin NUSUK Masar, inda ya ce hakan na nufin cewa daga cikin kujerun 95,000 da aka saba samu, yanzu mahajjata 51,513 daga jihohi da jami’ai za su tafi, yayin da sauran 15,397 za su kasance na kamfanonin yawon buɗe ido.

Elegushi ya bayyana cewa Saudi Arabiya ta rage wannan adadi saboda samun tara a kujerun bara, inda kuma ya ce rabon kujeru zai dogara ne da yadda kowace jiha ta yi amfani da nata wajen aikin Hajjin 2025.

A nasa ɓangaren, mamba a kwamitin gudanarwar NAHCON kuma mai wakiltar ma’aikatar lafiya, Dakta Saidu Dumbulwa, ya jaddada cewa Saudiyya ta kafa ƙaƙƙarfan dokar tantance lafiyar mahajjata.

Ya ce ba za a bari masu cutar hanta ko koda, masu tabin hankali, cutar sankarau, ciwon daji, tarin fuka ko masu juna biyu su shiga ƙasar ba.

Wannan mataki, a cewarsa, yana da nufin rage haɗarin yaduwar cututtuka da kuma rage nauyin kiwon lafiya ga hukumomin Saudiyya.

Haka kuma, ya ce tantance lafiyar mahajjata za ta kasance a asibitocin da aka amince da su kawai, inda za a sa hannu ta hannun manyan likitoci na jihohi domin kauce wa bogi.

Ya kara da cewa an kafa tsarin da zai danganta fitar da visa da takardun lafiya da za a tantance a shigar ƙasar Saudiyya.

A wani bangare kuma, kwamishinan NAHCON mai kula da manufofi, ma’aikata da kuɗaɗe, Aliu AbdulRazak, ya bayyana cewa hukumar ta samu amincewa wajen tura kuɗaɗen jihohi kai tsaye zuwa babban bankin ƙasa (CBN) akai-akai domin amfana da sauyin farashin musayar kuɗi.

Shi ma wakilin babban bankin ƙasa a hukumar, Dakta Adetona Adedeji, ya ce zai sanar da CBN bukatar NAHCON ta rage kaso biyu cikin ɗari na kuɗin da ake cirewa daga asusun mahajjata.

Shugaban hukumar NAHCON Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce suna ƙoƙarin tattaunawa da hukumomin Saudiyya don rage wasu kuɗaɗen da ake biya, kamar na ɗaukar kaya, domin rage nauyin da ke kan mahajjata.

Sai dai ya ce ba za a rage kuɗin masu ba da sabis ba, domin hakan zai iya shafar ingancin ayyukan da mahajjata za su samu.

NAHCON ta kuma tunatar da jihohi kan ranar ƙarshe ta tura kuɗin mahajjata, wadda aka sa ranar 21 ga Disamba, tana mai shawartar su da su tabbatar da isowar kuɗi kafin lokacin.

Hukumar ta sanar da cewa za a yi amfani da tsarin kayayyakin tafiya na ƙasashen duniya, inda kowanne mahajjaci zai iya ɗaukar jakunkuna biyu masu nauyin kilo 23 kowanne, da kuma ƙaramar jaka ɗaya a hannu.

Shugaban taron shugabannin hukumar alhazai na jihohi, Alhaji Idris Almakura, ya jaddada muhimmancin wannan rage kujeru, yayin da sakataren hukumar alhazai ta jihar Adamawa, Dakta Abubakar Salihu, ya yaba da yadda NAHCON ke haɗa jihohi a shirye-shiryen aikin Hajji.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here